An harbe mahaifin hakimin kauyen Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a jihr Kano, Dahiru Abba.

Dan sa wanda shi ne Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Barista Munir Dahiru Maigari, ya tabbatar wa da Jaridar Daily Trust faruwar lamarin.
Maigari ya ce, abin ya faru ne da misalin karfe biyu na safe, suka zo suka yi abin da suka yi, yanzu suna shirye shiryen binne shi.

Ya kara da cewa ba za su iya cewa komai ba dangane da musabbabin abin da ya faru a yanzu, amma ya mutu kuma muna addu’ar Allah ya jikansa da rahama.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin gidan sarkin inda suka far masa kafin su bude wuta.
Ya bayyana cewa an yi jana’izar ne a gidansa da ke kauyen Maigari da safiyar Lahadi.