Ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya sun ce za a ci gaba da fuskantar ƙaraanci da wahalaar man fetur har zuwa bayan zaɓen gwamnoni a Najeriya.

Wahalar man fetur ta ƙara tsananta ne a ƴan kwanakin nan a Abuja da wasu jihohin arewacin Najeriya har kae siyar da lita guda a kan kuɗi naira 400 zuwa naira 50.


Maitaimakin shugaban ƙungiyar dillalan man fetur na ƙasa Abubakar Maigandi ne ya shaida hakan ya ce za a ci gaba da fuskantar ƙarancin man har zuwa makon gaba na bayan zaɓe.
Ya ce dalilin wahalar da ta haifar da karancin man shi ne yadda ake tsammanin za a iya fuskantar rikici a zaɓen gwamnoni wanda hakna ya sa su ka dakatar da motocinsu daga dakon man.
Sai dai ya ce bayan fahimta daa su ka yi na cewa babu wani rikici da za iya faruwa, nan da makon gaba man fetur na iya samuwa a yankunan da ake fuskantar ƙaranci da tsadar.
Wasu rahotanni sun ce masu dakon man ba za su yi aiki ba har lokacin da tattara sakamakon zaben gwamnoni da za a yi.
Rashin aikin da masu dakon man za su yi, na iya ƙara ta’azzara karanci da tsadar man fetur a kwanakin da ake tunkara.