‘Yan sanda sun hallaka wasu mutum 3 tare da cafke mutum 2 da ake zargi ‘yan bindiga ne a jihar Ebonyi.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, sanarwar ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sunyi nasarar kwato bindiga kirar AK 47 biyu tare da bindiga kirar gida guda 1 sai harsashen AK 47 guda 50 dai dai sauran muggan makamia daga hannun wadanda ake zargin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gargadi masu tayar da zaune tsaye a jihar da cewa basu da mafaka a jihar.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su zamto masu bawa jami’an su hadin kai da goyon baya da kuma bayanai domin dakile miyagun aiyuka a jihar.
