Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa reshen Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 17 uku su ka jikkata a wani hadarin mota da ya afku a kauyen Yaura da ke kan titin Wudil zuwa Bauchi da ke karamar hukumar Albasu a Kano.

Kwamandan hukumar Ibrahim Sallau Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sallau ya bayyana cewa hadarin ya faru ne da yammacin ranar Labara tsakanin wata mota kirar Honda Accord da kuma wata mota kirar karamar Bas.

Kwamanda ya ce masu ababen hawa da ke wucewa akan hanyar ne su ka sanar da jami’ansu da ke sintiri,inda su ka yi gaggawar tura jami’annasu gurin da lamarin ya faru domin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Ibrahim Sallau ya kara da cewa hadarin ya afku ne sakamakon gudun wuce sa’a da kuma aron hannu ba bisa ka’ida ba wanda hakan ya haddasa gaza sarrafa motar wanda hakan ya sanya daya motar ta daki dayar inda mota daya ta kama da wuta.

Hadarin ya rutsa ne da mutane 21 da ke cikin motoci biyun, yayin da maza manya 11 ke ciki mata manya biyar tare yaro karami daya dukkan su sun rasa rayukansu.

Sallau ya kara da cewa ukun kuma da su ka jikkata sun hada namiji babba daya mace babba daya da kuma karamin yaro namiji, inda aka kaisu da su Asibitin garin Wudil domin kula da lafiyar su, yayin da aka mika wadanda su ka rasa rayukansu ga iyalansu domin yi musu sutura.

Daga karshe kwamandan yayi kira ga masu ababan hawa da su kiyaye dokokin tuki domin kaucewa faruwar hadurra ko yaushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: