Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta gargadi ’yan Najeriya kan ci gaba da amfani da wasu magungunan ciwon ido da yanzu haka suke yawo a kasuwannin Najeriya.

Hukumar ta ce magungunan na EzriCare da kuma Delsam, da tuni aka bayar da umarnin kwashe su daga kasuwanni.
Umarnin daina amfani da magungunan na kunshe ne a wata sanarwa ga jama’a mai dauke da sa hannun Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, a Abuja a jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce an janye magungunan ne a watan Fabrairu bayan an sami rahotannin gurbatarsu da wani sinadari mai cutarwa ga lafiyar idanu.

Ta ce tun bayan sanarwar, Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka ta Amurka (CDC) ta bayar da rahoton yadda marasa lafiya 68 suka kamu da cuta, a Jihohi 16 na kasar.
A cewar Farfesa Mojisola, Sauran matsalolin da aka gano maganin na haddasawa sun hada da dauke gani gaba daya da cire kwayar idanu da kuma mutuwa sanadiyyar taruwar jini.