Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wani jami’inta mai mukamin Insfector Obi Abri bisa zargin laifin hallaka wani dan kasuwa a shingen duba ababen hauwa a kan titin Agabolu-illah dake birnin Asaban jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Edefe Bright shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na Twitter.
Rahotanni sun bayyana cewa mamacin sun sami hatsaniya ne da jami’in dan sandan bayan da ya nemi dan kasuwar ya bashi cin hancin amma ya bashi naira dari, saida jami’in ya nemi mutumin da ya kara masa kudi amma yaki wanda hakan ya hassala jami’in kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Sai dai daga bisani jami’in ya harbe dan kasuwar har lahira nan ta ke.

kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda zata tabbata da anyiwa iyalan mamacin adalci.