Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya kafa kwamiti mai mutane 41 wanda zai yi aikin tsare-tsare domin mika mulki ga sabuwar gwamnatin Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jihar Kabiru Balarabe ya fitar a ranar Alhamis.
Balarabe ya bayyana cewa tsohon ministan kudi Bashir Yuguda ne zai jagoranci kwamitin.

Sauran sun hada da sakatare a kwamitin Dr Lawan Hussaini babban sakataren harkokin Majalisar zartarwa a ofishin gwamna mai ci da sauransu.

Kamfanin dillancin labaran Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa kwamitin zai yi aikin tabbatar da mika mulki ga sabuwar gwamnatin Jihar cikin tsari tare da samar da bayanan da su ka dace ga sabuwar gwamnatin.
Za dai a rantsar da sabbin shugabannin a Najeriya ciki harda shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, inda a Jihar ta Zamfara za a rantsar da Dauda Lawal a matsayin sabon gwamnan Jihar.
Akalla mutane da dama ne su ka rasa rayukan su a yayin barkewar fadan kabilanci a tsakanin ‘yan kabilar Kuteb da Fulani a cikin karamar hukumar Ussa ta Jihar Taraba.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa ba a san musabbin tashin rikincin ba amma wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ‘yan kabilar Kuteb ne su ka zargi fulani da kai hari akan ‘yan kabilar ta Kuteb wanda hakan ya hadda tashin rikicin tare da yin garkuwa da wasu.
Shaidan ya ce hakan ne ya sanya ‘yan kabilar ta Kuteb su ka kaiwa Fulanin hari a Kwe Sati wanda hakan ya sanya fadan ya tsallaka Fikye ranar Alhamis a Jihar.
Shugaban Kungiyar Kabilar ta Kuteb Emmanuel Ukwen ya shaidawa Daily Trust cewa a yayin rikicin mutane da dama ne su ka rasa rayukan su daga kowacce kabila.
Ya kara da cewa fadan ya haifar da kone gidaje da dama yayin da mutanen yankin su ka tsere.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa an kone fadar Sarkin Lisam Kwe Ando Madugu bayan zargin shi da ake da marawa Fulani baya.
A yayin da aka tuntubi shugaban kungiyar miyatti Allah na karamar hukumar Alhaji Bello bai ce komai ba a halin yanzu.
A cikin makon da muke bankwana da shine dai shugaban karamar hukumar ta Ussa Abershi Musa ya sauka daga kan mukamin sa bayan ya zargi gwamnatin Jihar da gaza daukar mataki akan yawaitar asarar rayukan da ake a Jihar inda kuma ya zargi Fulani da aikata barnar.