Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a, 21 da Litinin 24 ga watan Afrilun 2023 a matsayin ranakun hutu domin shagulgulan Sallah Karama ta bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar, Dokta Shuaib Belgore, a madadin gwamnatin.

Ministan ya kuma yi amfani da damar wajen taya daukacin al’ummar Musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya.

Aregbesola ya kuma yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan halaye kanar tausayi, kaunar juna, yafiya, zaman lafiya, sadaukarwa da sanin hakkin mamkwabta da Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a shirye yake ya mika mulki ga zababbiyar gwamnati mai jiran gado bayan da aka kammala zabe cikin nasara.

Aregbesola ya ce gwamnati za ta ci gaba da iya bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin dukkan ’yan kasa da ma baki da ke zaune a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: