Biyu daga cikin yan matan Chibok da mayakan kungiyar boko haram su ka yi garkuwa da su a jiihar Borno sun tsere daga hannunsu bayan tsawon shekaru.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana sun nuna cewa yan matan biyu sun shekaru akalla 2 a hannun mayakan sun samu damar kubuta daga yan boko haram.

Yan matan wadanda yan makarantar Chibok ne aka yi gakuwa da su tun shekarar 2014 kafin disashewa boko haram kaifi a Najeriya.

Sai dai jefi-jefi jami’an tsaro sukan samu damar kubutar da wasu a lokaci bayan lokaci duk da daliban na da yawa a wurin yan boko haram.

koda a shekarun baya sai da yan boko haram su ka je wani gari kusa da sambisa inda suka ajiye wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: