Mai garin Chida da a ka yi garkuwa da shi a watan daya gabata ya shaki iskar yanci bayan biyan kudin fansa

.Mai garin Chida da ka yi garkuwa da shi a ranar takwas ga watan da ya gabata na Afrilu tare da yayansa Uku da kuma karin ma’aikatansa tara sun shaki iskar yanci.

Daya daga cikin yayansa kuma daya cikin wadanda aka yi garkuwar Ishaka ya bayyana cewa sai da aka biya kudin fansa kafin sakin mahaifin nasu.

Ya ce kafin mahaifin su da sauran wandan da aka yi garkuwa da su su shaki iskar yanci sai da aka bayar da kudi kimanin miliyan bakwai.

Dan shugaban yankin Kwali Ishak ya ce yan garkuwar sun saki babban su a ranar Talata tare sauran wadanda aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Toto jihar Nassarawa.

Sai dai rundunar yan sandan jihar ta Nassarawa ba ta bayyana wata masaniya ba game da lamarin bayan shakar yanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: