Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ba zai karba ba, ko an nada shi Ministan Babban Tarayya ba a Gwamnatin Bola Tinubu da za a rantsar ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a yayin da ake shirye-shiryen rabon mukamai a sabuwar gwamnatani, inda ake hasashen za a nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Ko a bashi ministan Abuja ba zan karba ba.

Ya ce ya sha fada cewa ba zai maimaita mukamin da ya taba rikewa a baya ba alhali akwai akwai matasan da suka fi dacewa da kujerar.

Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa, ba zai koma gidan jiya ba.

Ya ce tun da ya bar Abuja bai sake komawa ba sai a shekarar 2016 da aka nada abokin karatun sa a matsayin minista, ya bukaci ganin sa.

Ya ci gaba da cewa, nan da kwana 19 zai bar Kaduna, kuma ba zai kara zuwa ba sai idan ya zama dole.

Ya ce shi ba ya ma tunanin kujerar ministan Abuja, ya gama da ita kuma ba zai ce komai kan ayyukan wadanda suka yi bayani ba.

El-Rufai, ya ce, wanda ke cikin mutanen da suka yi tsayuwar daka wajen ganin mulki ya koma yankin Arewa bayan wa’adin Shugaba Buhari, wanda hakan ya kai Tinubu ga nasara, ya ce ya fi karfin kujerar minista.

A zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, gwamnan ya kasance ministan Abuja, inda ake ganin ya yi rawar gani wajen zamantar da birnin da kuma samar da cigaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: