Hukumar zaɓe mai zama kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano ta ce ta kammala aikin zaɓen shekarar 2023 da aka shirya.

 

Shugaban hukumar Ambasada Abdu Abdusdamad Zango shi ne ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a helkwatar hukumar yau Alhamis.

 

Ya ce dukkanin ayyukan da aka ɗora musu don ganin sun shirya tare da sanar da sakamakon zaɓe sun yi shi cikin kwanciyar hankali, amana da kuma gaskiya.

 

Ya kara da cewa hukumar ta fahimci darrusa da dama dangane da zaɓen da aka gudanar wanda hakan ke zama ilimi domin tunkarar zaɓe na gaba.

 

A nasu bangaren jami’an yan sanda a jihar sun ce sun shirya domin daƙile duk wani yunkurin na hana mika mulki ko kawo cikar yayin bayar da mulki.

 

Kwamishinan su a Kano Usaini Gumel ne ya yi ƙarin haske a dangane da shirin da su ke yi don ganin sun tabbatar da an gudanar da miƙa mulki ba tare da matsala ba.

 

Hukumar zaɓe ta INEC a Kano ta sha yabo daga kungiyoyi daban-daban da ƴan siyasa a kan zaben shekarar 2023 da aka yi.

 

Duk da cewar masu yi wa ƙasa hidima sun koka a kan rashin biyansu kudadensu, sai dai hukumar ta ce ta biya mafi yawa daaga ciki kuma wadanda ba a biya ba mutane ne wadanda su ke da matsala a bankinsu ko kuma ba su bayar da bayanansu daidai ba ko kuma bankin da su ka bayar ba shi da sahalewa da babban bankin ƙasa na CBN.

 

Yaron ya samu wakilcin mai maartaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, jami’an tsaro, shugabannin jamiyya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: