Shugaba Najeriya mai barin gado Muhammadu Buhari ya ce ya matsu kwana shida su cika saboda ba zai iya jure matsin lamba da yake fama da shi ba.

Buhari ya fadi haka ne a yayin taron cin abinci don karrama shi a ranar Talata 23 ga watan Mayu a Abuja wanda jami’an sojin kasar suka shirya.
Manema labarai sun ruwaito cewa Buhari wanda ya je wurin taron ya bayyana rashin zuwan nashi da wuri akan matsin lamba da yake samu yayin barin mulki.

Ya kara da cewa a kwanakin nan yana fama da matsin lamba da kuma jerin tarurruka da kuma abubuwan da yake son kammalawa kafin barin mulki.

Shugaba Buhari wanda ya jagoranci taron majalisar zartaswa, ya kuma kaddamar da ayyuka da dama da suka hada da kaddamar da ofishin jami’an yaki da fasa kwauri na kwastam kafin wannan taro inda ya nemi afuwa da su masa uzuri.
Buhari ya godewa jami’an tsaro saboda sadaukarwarsu ga tsaron kasa, ya bukace su da sauran jami’an tsaro da kada su gaji wurin tabbatar da tsaro a fadin kasar.