Gwamnati tarayyar Najeriya ta ce ta amince Jama’a sun dinga yin amfani da katin cirar kudi mai hade da bayanin katin dan kasa wato komai da ruwanka.

Katin wanda za a dinga amfani da shi wajen cire kudi da kuma bukatar amfani da katin dan kasa idan ta zo.

Ministan sadarwa da tattalin Arziki a Najeriya Isah Ali Ibrahim Fantami ne ya bayyana haka a zaman majalissar zaratarwa da aka yi a jiya Laraba.

Cikin kudirin da Fantami ya mikawa Buhari ya na so ya zamana mutum zai iya amfani da katinsa wajen cirar kuma shi ne na dan kasa wanda bakuna za su fara yi.

Bayan da shugaba Buhari ya amince da kudirin Farfesa Fatami ya sanar tare da cewa bakuna idan mutum ya so za su yi masa hakan ba tare da ya biya ko sisi ba.

Sannan Fantami ya ce an kuma nemi yarjewar hukumar dake kula da katin dan kasa don bayar da dama, wanda za a fara ba da jimawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: