Wasu mahara a Jihar Imo sun hallaka wani basaraken Orsu Obota Eze Victor Ijioma a karamar hukumar Oguta ta Jihar .

Maharan sun hallaka ba sakaraken ne a yankin Isama da ke gundumar Mgbele a cikin karamar hukumar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa masu sarautar gargajiya biyu ne aka hallaka a hare-hare daban-daban da aka kai yankin a ranar Alhamis.

Rahotannin sun tattaro cewa ‘yan bindigan sun tsare basaraken a lokacin da ya ke tsaka da tafiya a kusa da garin Izombe inda su ka hallaka shi daga bisani su ka kone gawarta sa.

Bayan hallaka masu sarautar gargajiyar biyu da ‘yan ta’addan su ka yi hakan ya tilastawa mazauna yankunan da lamarin ya faru tsere daga muhallan su.

Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Henry Okoye ya bayyana cewa bashi da cikakken bayani akan faruwar hare-haren,inda ya ce bayan Sun kammala bincike za su fitar da cikakken bayani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: