Rundunar Sojin kasa Najeriya ta bayyana cewa ta hallaka mayakan Kungiyar ta’adanci ta ISWAP 55 tare da manyan kwamandojin su a jihar Bornon.

Cikin wata sanarwa da hukumar Sojin ta fitar a jiya Talata ta ce Sojojin MNJTF bisa Operation Zuma suka hallaka mayakan.

Ta ce an samu nasarar ne a cikin kwanakin 22 farawa daga shida ga wata mayu Lahadi 28 ga wata.

Su ka ci gaba da cewa cikin Operation Harbin Zuma wanda aka tanada domin kauda yan ta’adda a Najeriya.

Hare-haren dai da a lokatan an yi nasara hallaka mayakan har 55 da manyan kwamandoji a yankunan Arege Malam Fatori karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Manyan kwamandoji sun hada Fiya Abuzeid da Qaidu Abou Omama da kuma Qaid malam Mustapha a cikin tawagar manyan kwamandoji.

Sannan Sojin sun samu damar Motoci 13 da kuma mashina 13 da wasu kayyaki.
Sai dai jami’an Soji hudu sun rasu a harin sai wasu da suka jikkata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: