Sabon gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, ya soke naɗin manyan sakatarori 23 da manyan daraktoci 15, da gwamnatin da ya gada ta Aminu Waziri Tambuwal, ta yi.

Gwamnan wanda ya fara aiki a ranar Talata, ya kuma dakatar da masu riƙe da sarautun gargajiya 14 da gwamna Tambuwal ya naɗa a jihar.

Masu riƙe da sarautun gargajiyar sun haɗa da dagatai 13 da kuma Magajin Garin Sokoto, Alhaji Sama’ila Abdulkadir Mujeli.

Dagatan sun haɗa da Alhaji Aliyu Abubakar III (Ciroman Sokoto) da dagacin Sokoto ta Arewa, Alhaji Buhari Dahiru Tambuwal, Sarkin Tambuwal, Alhaji Ibrahim Dasuki Muhammadu Maccido (Barayan Zaki), dagacin Sokoto ta Kudu.

Sauran su ne Alhaji Ibrahim Bello Dansarki, Marafan Tangaza, Alhaji Bello Sani Torankawa, Sarkin Yamman Torankawa.

Ba a bayyana dalilin dakatar da su ba, amma wani mamba a kwamitin miƙa mulki wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya bayyana dalilin dakatar da su yana da nasaba da rawar da suka taka a lokacin zaɓen da ya gabata.

Kakakin gwamnan jihar, Abubakar Bawa, a yayin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar, ya bayyana cewa za a sake duba kan naɗin da aka yi musu nan bada daɗewa ba domin ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: