Babbar Kotun tarayya da ke Jihar Legas ta aike da wani jami’in dan sanda zuwa gidan ajiya da gyaran hali na Jihar bisa zargin sa da aikata damfarar kudade har Naira miliyan 128.

Kotun ta zargi Jami’in mai suna DSP Jerry Ogunsakin da hada baki da kuma damfarar wani dan kasuwa kudi Naira miliyan 128.

Dan sanda mai gabatar da kara, Chukwu Agwu, ya shaida wa kotun cewa Jami’in tare da wasu mutum biyar ne suka ha Inci dan kasuwar da ke neman canjin Dala, cewa su ’yan canji ne kuma suna da Dala ta Naira miliyan 128 da yake nema.

Mai gabatar da karar ya ce bayan dan kasuwar ya basu kudin tun a watan Nuwambar shekarar 2022 mutanen su ka tsere ba tare da sun ba shi ko da Dala daya ba.

Dan Sandan mai shigar da karar ya ce sauran mutum Biyar din dai da su ka yi damfarar ba a samu nasarar kama su ba,inda kuma jami’in dan sandan da aka gurfanar a gaban Kotun ya musanta zargin da ake yi masa.

Bayan sauraran karar Kotun ta bayar da umarnin ai kewa dashi gidan gyaran hali tare kuma da dage sauraron Shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Yuni da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: