Kotun sauraron kararrakin zaben da ke birnin tarayya Abuja ta amince da shaidar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gabatar mata.

Kotun ta karbi takardun shaidar ne a ranar Juma’a wanda suka hada da takardar shaidar bautar kasa da na kammala digiri da kuma takardar shaidar aiki na kamfanin Mobil Oil Nigeria Plc.
Jam’iyyar PDP ta gabatar da shaidar ne ta hannun Mike Enahoro Ebah wanda ya ce takardun Tinubu ne ya karbe su amma suna dauke da sunan Bola Adekunle Tinubu.

Jagoran lauyoyin jam’iyyar ta PDP Chris Uche ya bayyana cewa mai bayar da shaidar ya kuma gabatar da wasu takardu da kuma wasika zuwa ga hukumar zabe.

Lauyan hukumar zabe Abubakar Mahmud da lauyan Tinubu Emmanuel Ukala da kuma lauyan APC, Lateef Fagbemi dukkansu sun ki amincewa da shaidun da jam’iyyar ta PDP ta gabatar.
Atiku ya gabatarwa da kotun shaidun ne akan kalubalantar shugaban Najeriya Bola Tinubu kan mallakar takardun bogi da sauran zarge-zarge da ya ke yi masa.
Shugaba Tinubu dai na fama da korafe-korafe tun bayan ya zama gwamnan jihar Lagos a shekarar 1999.
Mafiya yawan korafe-korafen da Atiku ya ke yiwa Tinubu sun hada da hanyar arzikinsa da rashin lafiyasa da kuma zargin cin hanci.
Sauran sun hada da zargin safarar kwayoyi da mallakar takardun bogi da sauransu.
