Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya taya alummar Musulmin Najeriya murnar gudanar da idin babbar sallah.

Tinubu ya bayyyana haka ne yau Laraba bayan ya gudanar da idin babbar sallah a birnin Legas.
Tinubu ya ce ya san kalubalen da yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Kuma kalubale ne mai tarin yawa amma za a magance shi.

Tinubu ya ce Allah baya dorawa bawansa abin da ba zai iya ba, don haka Allah ya san halin da Najeriya ke ciki Kuma za ta gyaru da yardarsa.
Ya ci gaba da cewa da yawan matsalolin Najeriya Tinubu ya ce ya gano su kuma ya fara magance wasu da dama ta hanyar shawarwarin masana kasar.
Tun da kasa ce ke da kalubale da dama bangaren tsaro da tattalin Arziki .
Tinubu ya bayyana hake ne yayin da ya cika kwanki 29 akan karagar mulkin Najeriya.