Wata kotu dake zamanta a jihar Kano ta aike da wani dan Jaridar bogi da lauya izuwa gidan gyaran hali da tarbiyya.

Alkalin kotun shari’ar Abdulmumini Gwarzo shi ne ya Yanke hukunce a kotunsa da ke karamar hukumar Kiru a jihar Kano.
Alkalin kotun ya daure Wanda ake zargin mai suna Zaharaddini Sani Mai Doki izuwa gidan gyaran halin na tsawon watanni 15 bayan ya amsa tuhumar da ake masa.

Tuhumar da ake masa sun hada cewa shi dan Jarida ne da kuma cewa shi lauya ne tare da yunkurin kare wasu mutane a kotu

.
A yayin zaman Wanda ake zargin mazaunin jihar Kaduna ne bayan ya bayyana kansa shi a matsayin lauya ne Kuma dan Jarida.
Sai dai mai Shari’a Malam Abdulmumini ya tura sakon tabbatar da Wanda ake zargin izuwa Kungiyar lauyoyi ta jihar Kaduna domin tabbatar da shi lauya ne ko akasin haka, sai su ka bayyana cewa ba su San shi ba.
Daga bisani mai Shari’a ya yi amfani da sashi na 303 tare mika shi gidan gyaran hali na watanni 15 tare da biyan tara 20,000.