Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta jita-jitar da ke yadawa cewa ta janye jami’anta masu kula da wasu tsofaffin jami’an gwamnatin Kasar.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana cewa mutane su yi watsi da sanarwar da ake yadawa ba.

Sanarwar ta kara da cewa sanarwar dakatarwar da aka fitar na nuni da cewa na dauke da sanya hannun mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai mukamin DCP wanda shi kawai zai nuna musanta labarin ne.

Yayin da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai mukamin ACP ne ya yadace ya sanya hannu.

Mukaddashin Sufeton yan Sandan na Kasa Kayode Adeolu Egbetokun ya bayyana cewa za su gudanar da bincike domin gano waɗanda suka fitar da sanarwar domin su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: