Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kama wasu makamai masu tarin yawa a yayin da ake kokarin shiga da su Jihar Anambra.

 

Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Twitter na rundunar.

 

Kakakin ya ce jami’an bataliya ta 192 ce ta samu nasarar kama makaman a ranar asabar din da ta gabata.

 

Onyema ya bayyana cewa jami’an sun kama makaman ne da taimakon bayanan sirri da su ka samu.

 

Mai magana da yawun rundunar ya ce an kama kayan ne akan titin Ajilete zuwa Owode da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa da ke Jihar Ogun, inda suka kama manyan bindigogi da harsashi mai yawa a cikin wata babbar mota.

 

Onyema ya ce mutanen da aka kama sun hada da Mista Eric Seworvor dan kasar Ghana da kuma direban motar Lukman Sani wadanda suke taimakawa jami’an wajen gudanar da bincike akan makaman.

 

Kakakin ya kara da cewa a yayin binciken da su ka gudanar sun gano cewa mutanen sun dauko makaman ne daga kasar Mali, inda suka biyo da su ta iyakar Idiroko kan hanyarsu ta zuwa Onitsha ta Jihar Anambra kafin a kamasu.

 

Onyema ya kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da bai’wa jami’an bayanan sirri domin kawo karshen batagari a Kasar.

 

A yayin mika gidiyarsa Shugaban sojin Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yabawa jami’an tare da yin kira garesu da su kara dagewa wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin


al’ummar Kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: