Wata babbar kotu a jihar Anambra ta yankewa wani ma’aikacin hukumar tattara haraji hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun ta yankewa mutumin hukuncin ne bayan ta sameshi da hannu wajen kisan wani ɗan kasuwa a jihar mai suna Ndubuisi Nwokolo.


An gurfanar da mutumin a gaban kotu a shekarar 2019 kuma ya aikata laifin a shekarar 2018 a ranar da aka hana hayar babur da aka fi sani da Acaɓa a Onitsha.
Mutumin ya ɗauki ɗan kasuwar a babur ɗin haya da nufin kaishi, sai dai ya saukeshi a tare da caka masa wuƙa wanda hakan yay i silar mutuwarsa.
Alƙalin kotun Justice D.A Onyefu ya karanta tuhumar da ake yi wa Ikanda tsakanin hukumar shari’a ta jihar bisa kisan da ya aikata.
Iyalan mamacin na ta kira don ganin an yi musu adalci wajen hukunta wanda aka kama.
Daga cikin bayanan da aka gabatarwa kotun an tabbatar da cewar Ikanda ya tsere bayan ya aiakta alaifin sai dai a shekarar 2019 an kamashi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.