Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya sun fara yajin aikin gama gari a yau Laraba.

 

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Dakta Orji Emeka ne ya sanar da fara yajin aikin a daren ranar Talata bayan sun yanke hukunci.

 

Ya ce majalisar zartarwa na ƙungiyar sun yanke shawarar tafiya yajin aikin a yayin wani zama da su ka gudanar a jihar Legas.

 

Daga cikin dalilan fara yajin aikin akwai buƙatar basu haƙƙoƙinsu na horo, da kuma batun albashinsu.

 

Ƙungiyar ta sha tafiya yajin aiki a baya tare da buƙatar gwamnatin tarayya ta biya musu buƙatunsu domin cigaba da aiki yadda ya kamata.

 

A baya an ruwaito yadda likitoci su ka fice daga ƙasar tare da tafiya ƙasashen ƙetare domin yin aiki.

 

Sai dai majalisar dokokin ƙasar ta ce wajibi ne kowanne likita kafin ya fita ƙasar waje don yin aiki sai yayi aiki na tsaron shekaru biyar a Najeriya.

 

Dokar da ƙungiyar su ka ce ba su aminta da ita ba.

 

 

 

 

 

Break

 

 

 

Aƙalla sojoji Bakwai ne su ka rasa rayuwarsu yayin da aka hallaka farar hula da dama a wani sabon hari da ƴan bindiga su ka kai jihar Zamfara.

 

Harin ya faru a yammacin ranar Litinin a Kangon Garacce da ke Dangulbi a ƙaramar hukumar Maru ta jihar.

 

Wani mai suna Lawal Ɗangulbi ya shaida cewa jami’an sojin na kan hanyarsu bayan sun samu kira a kan harin da ƴan bindiga su ka kai garin kuma a kan hanyarsu ne su ka buɗe musu wuta.

 

Ya ce ƴan bindigan sun kasa kansu wuri daban-daban yayin da wani rukuni daga ciki su ka shiga garin wasu kuwa su ka tsaya a bayan gari.

 

Sojojin bakwai ne su ka rasa rayuwarsu yayin da aka hallaka farar hulka aƙalla Ashirin a garin.

 

Jihar Zamfara na fama da hare-haren ƴan bindiga tsawon lokaci wanda hakan yay i silar raba mutane da dama da muhallinsu tare da rasa rayuka masu yawa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: