Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godwill Akpabio ya tabbatar da cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayen mutum 28 da yake neman a tantance domin naɗasu a a matsayin Ministoci a gwamnatinsa.

Daga cikinsu akwai Nasiru Ahmad El_Rufa’i Tsohon gwamnan Kaduna Wanda Kuma Tsohon Ministan Birnin tarayya Abuja ne.

Sai Nelson Wike Tsohon gwamnan Jihar River’s.
daga Jihar Jigawa akwai Badaru Abubakar sai Ahmad Dangiwa da Hannatu Musawa daga Jihar Katsina.

Daga cikin sunayen da Shugaban ya aikewa Majalisar akwai jihohi 11 da Basu samu wakilci ba da suka hada da Kano, Lagos da Kuma Jihar Adamwa.

Ana saran Shugaba Bola Ahmad Tunubu sai sake turawa Majalisar jerin sunayen Ministoci Kashi na biyu zuwa wani lokaci.

Tunudai al’ummar Kasa suka fara Taya murna ga sabbin Ministocin duk kuwa da cewa majalisa ba ta Kai ga tantance su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: