Tun bayan lokacin da aka kama Nnamdi Kanu daga Kasar Kenya, kungiyar IPOB ta gudanar da zanga-zanga daban-daban da daukar haramtattun matakai ciki har da aiwatar da dokar zama a gida a duk ranakun Litinin har sai an sako Nnamdi Kanu.

Masana da dama na ta tofa albarkacin bakinsu a kan tasirin da matakin ya yi musamman a yankin Kudu maso Gabas da ma kasa baki daya.


Har ila yau a bangaren Gwamnatin Tarayya, musamman yanzu da aka tabbatar da nadin sabbin manyan hafsoshin tsaro, an fara daukar mataki a kan ‘yan haramtacciyar kungiyar ta IPOB.
Sabon salon da IPOB ta zo da shi domin matsin lambar a saki shugabanta tun daga ranar 9 ga Agustan 2021 ta yi tsanani a yankin Kudu maso Gabas, har ta kai ga rabuwar mazauna yankin da wasu ‘yan’uwansu.
A halin yanzu Litinin ta zama wani bangare na karshen mako.
Bankuna, shaguna, kamfanonin sufuri, coci-coci, makarantu da ofisoshin gwamnati dukkan su a kulle suke kasancewa.
Wani masanin tattalin arziki, Dakta Dozie Okeke, ya shaida wa manema labarai cewa, ba za a iya kididdige mummunar tasirin da wannan doka ta zaman gida ta haifar ga tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas ba.
A watan da mu ke ciki wata kotu ta bayar da umarnin ga hukumaar tsaro ta DSS da su bai wa Nnamdi Kanu damar ganawa da likitocinsa.