Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura ta ƙasa reshen jihar Imo ta dakatar da wnai jami’inta bayan da ya bi ayarin masu yajin aiki da zanga-zanga d ƙungiyar ƙwadago ta shirya.

Kwamandan hukumar a jihar Evaristus Ebeniro ne ya sanar da haka tare da tabbatar da cewar ba za su lamunci hakan ba.
Hukumar ta ce jami’in da ta dakatar ba ya daga cikin mutanen da za su yi aiki na musamman hakan ya sa su ka dakatar da shi domin fitar da yayi ta saɓa da doka.

Kwamandan ya barranata hukumar ta abinda jami’in ya yi tare da cewar yayi ne bisa raɗin kansa ba da yawun hukumar ba.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ƙungiyarb ƙwadago a Najeriya NLC ta shirya yajin aiki da zanga-zanga a faɗin ƙasar.
.
Ko da yake ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan shiga tsakani da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayi da kuma majalisar dokoki ta ƙasa.