Awannni kaɗan bayan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aikewa majalisar dokokin ƙasar neman sahalewar aike da dakarun soji zuwa ƙasar Nijar don ƙace mulki daga hannun sojin, shugaban ya fara shan suka ta ko ina a kan batun.

Ƙungiyar ECOWAS ta ce ba ta da waniz aɓe da ya rage illa amfani da ƙardin soja wajen karɓe ikon mulkid aga hannun sojin ƙasar Nijar, batuhn da wasu ƴan Najeriya ke yin watsi da shi.
Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta barranta kanta daga amincewar hakan tare da kira domin samun wata mafitar maimakon amfani da soja wajen karɓar mulkin.

Ko a ɓangaren malamai a Najeriya daban-daban na bayyana rashin dacewar hakan domin hakan na iya haifar da wata ƙiyayya da matsalar da ba a san ƙarshenta ba.

Dakta Snai Umar Rijiyar Lemo a Kano na daga cikin malaman da su ka soki batun tare da nuna rashin goyon baya a kai.
Mutane na kira ga shugaban ƙungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da a sauya dabara, domin amfani da ƙarfin soja wajen ƙwatar mulki a Nijar ba mafita ba ce.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar majalisar a wata wasiƙa da ya aike musu a ranar Alhamis, wanda kuma shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karantata.
Ƙungiyar ECOWAS na nemo dabarun ƙace mulki, bayan da masu mulki a Nijar ɓangaren soja su ka hyi watsi da tayin sulhu da wakilcin su ka je garesu a ranar Juma’a.