Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce za ta gudanar da zɓen cike gurbi na wasu ƴan majalisar dattawa a ƙasar.

Shugaban hukumar na ƙasa Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka bayan da aka aike da sunayen mutanen a matsayin ministocin da ake son naɗawa.

Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana haka a jiya Juma’a yayin wani taro da kwamishinonin zaɓe na jihohi da ya gudana a jihar Legas.

Kujeru huɗu biyu na majalisar wakilai da kuma wasu biyu na majalisar dattawa za a yi zaɓen cike gurbinsu a jihohinsu.

Zuwa yanzu hukumar na da zaɓen cike gurbi na kujeru Takwas kamar yadda shugaban hukumar zaɓen ya bayyana.

Ya ce wannan ma wata damar ce ta hukumar domin sake gudanar da sahihin zaɓe a jihohi daban-daban.

Jihohin da za a yi zaɓen sun haɗa da mzaɓun Surulere a jihar Legas, Jalingo Yaransi na jihar Taraba, Chibok a jihar Birno, da kuma mazaɓar Chikun a jihar Kaduna.

Waɗanann mazaɓu ne za a yi bayan da shugaban Najeriya ya aike da sunayensu a matsayin waɗanda yake son naɗawa ministoci.

Sauran zaɓukan kujerun za a yi ne a jihohin Imo, Kogi, Bayelsa wanda za a yi a watan Nuwamba na shekarar da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: