Wani jigo a jam’iyya mai mulki ta APC Uche Nwosu ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ba zai hana tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso dawowa jam’iyyarsu ta APC ba.

Uche ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar goyon baya da ya kaiwa shugaban jam’iyyar Dr Abdullahi Umar Ganduje a Abuja.
A yayin jawabinsa Uche ya ce Ganduje ba zai hana duk wani mai sha’awar shiga jam’iyyar tasu ta APC shiga ba.

Nwosu ya kara da cewa Ganduje zai yi farin ciki idan mutane na shiga jam’iyyar wanda hakan ka iya karawa Jam’iyyar ta APC ci gaba.

Ya ce shigar Kwankwaso APC zai taimakawa Ganduje a Kano kuma hakan ka iya haifar da sulhu a tsakaninsu.
Kazalika ya ce yin sulhun Kwankwaso da Ganduje ka iya dawo da karfin dimukuradiyya a Najeriya.