Rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun tabbatar da sakin magajin garin Daura wanda aka yi garkuwada shi fiye da watanni biyu.

Magajin Garin Daura ya shiga hannun masu garkuwa da mutane ne a wata Laraba bayan ya dawo daga sallar magariba.
Inda suka fara harbin iska sannan suka sakashi a mota daga nan ba a ƙara jin ɗuriyarsa ba.

