Wani mai kishin jihar Kano Bello Yusif Gamandi ya koka a kan yadda tafiyar gwamnatin jihar Kano ke zama tamkar tafiyar hawainiya.

A cikin shirin Ciki da Gaskiya wanda Matashiya TV ta saba gabatrwa a ranakun Asabar, Bello Gamandi ya ce kamun ludayin gwamnatin Kano a iya cewa gwanda jiya da yau.
Gamandi wanda ya ayyana kansa a matsayin cikakken ɗan jam’iyyar NNPP kuma m ai aƙidar Kwankwansiyya ya ce sam tsarin tafiyar gwamnatin da muƙarrabansa gwamnan ba sa yin aikin da ya dace domin ciyar da jihar gaba..

Ya ce hatta hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar Kano KAROTA ba ta yin abinda ya dace, domin akwai ayyukan da gwamnatin da ta gabata ta yi, amma yanzu su ka koma ci barkatai.

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a Kano Nabulisi Abubakar ya ce barin tashoshi da aka yi na bakin tituna, hukumar na yin ƙoƙari don kawo gyara a kai, haka kuma ƙofa a buɗe ta ke ga duk wuraren da aka ga jami’ansu na yin abinda bai dace ba domin sanar da su ta yadda za a ɗauki mataki.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu hukumar na cigaba da wasu ayyuka a ƙarƙashin ƙasa, domin tsaftace aikin da kuma samar da daidaito a faɗin jihar.