Masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro a arewa maso gabashin Najeriya sun nuna damuwa a kan yadda yankin ke fuskantar sabuwar matsalar tsaro.

Wasu sun fara aikata miyagun ayyuka masu kama da na mayaƙa Boko Haram.

Taron wanda aka fara shi a yau kuma za a ɗauki tsawon kwana uku ana yin sa an fara kuma zai cigaba da gudana ne a jihar Borno.

Shugabannin tsaro na shiyyar sun ce akwai wasu mutane da ke aikata wasu abubuwa wanda makamantansu ne su ka haifar da Boko Haram a yankunan.

An shirya taron ne domin samar da mafita yadda za a yi wa tifkar hanci ganin yadda lamuran ke barazana ga tsaro a shiyyar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Mohammed Lawal Yusuf ya yi bayani cewar, ayyukan da wasu matasa ke aikatawa a jihar na kamaceceniya da yadda Boko Haram ta samo asali.

Za a shafe kwanaki uku ana gudanar da taron tare da duba yadda za a shawo kan matsalar kafin addabar yankin arewa maso gabashin ƙasar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: