Gwamantin jihar Kano ta ce za ta buɗe cibiyoyin koyon aikin sana’o’in dogaro da kai a jihar.

Sannan gwamnatin jihar Kano ta rage kashi 50 cikin ɗari na rijistar shiga manyan makarantu a jihar.
Ragin ya shafi iya ɗalibai ƴan asalin jihar Kano ne kaɗai.

A wata sanarwa da kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar Dakta Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce an yanke hukuncin ne yayin wata ganawa da da gwamnan ya yi da shugabannin manyan makarantu a jihar.

Sanarwar ta ce an yi haka ne domin baiwa ɗalibai a jihar damar samun ilimi.
Haka kuma gwamnatin za ta buɗe cibiyoyin koyon sana’o’in dogaro da kai a jihar yadda matasa za su tsaya da ƙafarsu.
Gwamnatin ta ce ta na mayar da hankali domin bayar da ingantaccen ilimi domin cigaban jihar.
Dukkanin ɗalibai da ke karatu a kwalejiji da jami’o’i mallakin jihar Kano kuma su ka kasance yan asalin jihar za su amfana da ragin kudin.
Bai wa ɓangaren ilimi muhimmanci na dga manufofin Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya sha alwashin haka tun lokacin yakin neman zaben sa.
