Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya dakatar da shugaban hukumar samar da kayan aikin gona a jihar.

Dakatarwar na zuwa ne bayan da aka hango gazawar shugaban bayan ɗorashi a muƙaminsa.

Gwamnaatin ta zargi shugaban aa karkatar da wasu kaya mallakin gwamnatin jihar.

A wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi.

An dakatar da Dakta Tukur Minjibir tun a ranar Talata 12 ga watan Satumba da mu ke ciki.

Sai dai sanarwar ta fita a yau Laraba.

Gwamnatin ta umarci dakataccen shugaban ya miƙa ragamar shugabancin ga babban nai mukami a hukumar.

Sannan gwamnatin ta ce za ta gudanar da bincike a kan zargin da ake yi a kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: