Ministan ilimi a Najeriya, Farfesa Tahir Mamman, ya jaddada yunkurinsa na tabbatar da ayyukan cigaba da za su daga likkafar bangaren ilimi a Najeriya.

 

Ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar ga kwamitin mataimakan shugabannin jami’o’in Najeriya a Abuja yau Laraba.

 

Mamman ya tabbatarwa da wakilan cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na da kyakkyawan yunkurin inganta harkokin koyo da koyarwa a daukacin jami’oin kasar nan.

 

Da yake nasa jawabin karamin ministan ilimi, Dr Yusuf Sununu, ya tabo batun matsalar rashin tsaro a jami’o’in Najeriya, wanda ya danganta batun da halin da ake ciki na garkuwa da aka yi da daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.

 

Karamin ministan ya tabbatar da kyakkyawan yunkurinsu na kwararan matakai da aka dauka domin shawo kan al’amarin.

 

A cikin jawabinta, jagorar tawagar kuma shugabar kwamitin, Farfesa Lilian Salami ta nuna godiya da farin cikinta ga ministan bisa kasancewarsa mutum na farko a tarihi da aka nada minista lokacin da yake kan matsayin mataimakin shugaban jami’a.

 

Ms Salami ta hakaito wasu kalubale sa jami’o’in kasar ke fuskanta da su ka hadar da rashin isassun kudaden gudanarwa, wadatattun ma’aikata da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: