Shuwagabannin kungiyar Kwadago ta kasa NLC ba su halarci taron da gwamnatin tarayya ta gayyacesu ba a jiya Juma’a.

 

Kamar yadda sanarwar ta fito daga gwamnatin tarayya ta gayyatar NLC zuwa taro don samun mafita a shirinsu na tafiya yajin aiki sai baba ta gani.

 

Sai dai shuwagabannin kungiyar Kwadago ba su halarci taron ba.

 

Kamar yadda wata sanarwar ta fito daga kungiyar Kwadago ta ce dalilin da yasa ba su halarci taron ba shi ne ba su samu cikakkiyar sanarwar ba a akan lokaci.

 

Su ka ce sun samu sanarwa da misalin karfe 10:00am na safe Kuma aka bayyana cewa za a gudanar da taron karfe 12:00pm na rana hakan kuwa ya sanya da yawa shuwagabannin kungiyar ba sa birnin Abuja.

 

Suka ce suna matukar son a samu daidaito da gwamnatin amma ita kuwa ba da gaske take ba.

 

NLC ta ci gaba da cewa gwamnati ta kan dauki lamarin su da wasa don shi ya sa ma suke daukar nauyin wasu kungiyoyin.

 

Sai dai har zuwa hada wannan rahotaon ba a ƙara jiyo ikirarin gwamnatin tarayya ba game da sanya wata ranar da za ta gana da ƙungiyar.

 

Sannan idan ba a manta ba a ranar uku ga watan Oktoba ne kungiyar Kwadago ke Shirin shiga yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasa Najeriya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: