Dangane da zargin kuma da akewa yan sanda na cin zarafin jama a babban sufetan yan sandan Najeriya ya bayar da umarni ga kwamishinonin da su bude wani sashe na musamman domin karbar irin wadannan korafin.

Sashin da ake Kira CRU sashi ne da aka Samar dabshi domin kai korafin yan sanda kuma za a iya gabatarwa ta hanyar kafar sanarwar zamani ba tare da zuwa ofis.


Rundunar yan sandan Najeriya ta sake jaddada shafinta na CRU don gabatar da korafin dan sanda mai cin zarafi.
Babban sufetan yan sandan Najeriya na kasa Egbetokun Olakayode ne ya bayyana haka ga manema labarai a babban birnin tarayyar Abuja.
Ya ce jama’a na ci gaba da korafi akan yan sanda masu cin zarafi hakan ya sa su ka sake jaddada shafin.
Ya ce don haka akwai shafi wanda aka samar don gabatar da dukkanin wani korafi in har wani jami’i ya ci mutuncin wani.
Sufeta Olakayode ya ci gaba da cewa ya bayar da umarni ga dakkanin kwamishinonin yan sanda da su Samar da wani sashe don yin hakan.
Daga karshe cikin bayaninsa ya ce ana samun sashen CRU har a kafar sadarwa ta internet ba tare da mutum ya je ofishin ƴan sanda ba
