Sabon shugaban hukumar Karota a Kano Baffa Babba Ɗan agundi ya shaidawa menema labarai cewa nan ba da jimawa ba za su ga yuwuwar hana tuƙa babur mai ƙafa uku a faɗin jihar baki ɗaya.

Alhaji Baffa Babba ya ce sun turawa jami an tsaro don gudanar da bbincike kasancewar matasa ne suka cika sana ar kuma da zarar sun kammala za su yanke hukunci.
Da yawa daga cikin matasa da magidanta ke amfana da sana ar wadda ta zama ruwan dare a faɗin jihar har ma da maƙota, sai dai mafi yawa hatsarirrika da ke faruwa cikin kwaryar birnin na da alaƙa da babur mai ƙafa uku.

