Majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya sun buƙaci a gwamnati da ta ƙara jami’an tsaron da za su bai wa manoma kariya.

A yayin da kaka ke ƙara gabatowa, majalisar ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara jami’an tsaro domin bai wa manoma kariya daga harin mayakan Boko Haram da masu garkuwa.


Kuɗirin ya fito ne daaga wakilin ƙananan hukumomin Chibok, Damboa da Gwoza a zauren majalisar Ahmed Jaha, wanda ya gabatar a ranar Talata.
Ƙudirin d aya shigar a majalisar ya bukaci da a kara yawan jami’an tsaro da za su baiwa manoma kariya ganin yadda kaka ke ƙara gabatowa.
Y ace hakan ne zai taimaka musu wajen amfanar noman da su ka yi.
Ƙudirin ya ce rashin bai wa manoma kariya zai danya a yi asarar dukiya.
Bayan gabatar da ƙudirin wakolin a zauren majalisar tarayya da ke wakiltar Jos ta Gabas da Jos ta Kudu a jihar Filato Dachung Musa Bagos ya mara baya tare da buƙatar jami’an tsaro na ganin sun bai wa manoma a Najeriya tsaro ba iya na wasu yankunan jihar Borno ba.
Majalisar ta karɓi ƙudirin tare da buƙatar baiwa manoma a Najeriya kariya wajen girbin amfanin gona.