Gwamnatin jihar Katsina ta amince da kashe kudi har Naira Miliyan 560, don siyo kayayyakin aiki da za a yaƙi matsalar tsaro a faɗin jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Nasir Danmusa ne ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da ƴan jaridu a jiya Alhamis.
Ya yi jawabin ne bayan fitowa daga zaman majalissar zartarwa na jihar inda ya ce, kayan aikin za a miƙa su ne ga sabbin jami’an tsaro da jihar ta ɗiba.

A kwanakin nan ne dai gwamnatin jihar ta ɗebi sabbin jami’an tsaro masu sanya ido kimanin mutane 1,500. Waɗanda dukkan su matasa daga sassan jihar dan kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro.

Danmusa ya ce “sahalewar da gwamnatin ta yi, ya zo ne gabanin bikin ɗiban jami’an tsaro mutum 1,500 wadanda zasu yi aikin sanya ido akan harkar tsaro a faɗin jihar.”
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN sun ruwaito cewa, garuruwan Ƙafur, Bindawa da Malumfashi an bayyana su a matsayin mafi muhimmanci, biyo bayan hare-haren ƴan ta’ addah da aka samu a kwanakin nan.