Rundunar ‘yan sanda Jihar Edo ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da hudu suka jikkata a wani hadarin jirgin kwale-kwale a Gelegele cikin karamar hukumar Ovia ta Jihar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa hadarin ya faru ne a yayin da jirgin ruwan, ya bugi wani jirgin da ke tsaye a bakin gaɓa ranar Alhamis da ta gabata.

Mafiya yawa daga cikin wadanda ke cikin Jirgin mata da kananan yara ne.

Shugabar karamar hukumar Blessing Perewari, ta ce wasu sun kubta da rayukansu, yayin da mutane Bakwai suka mutu.

A yayin ziyara da Blessing ta kai gurin da hadarin ya faru, ta jajantawa ‘yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Sannan ta ce tuni aka dauki gawarwakin mutanen da suka mutu zuwa dakin ajiyar gawarwaki na Jihar.

Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin ne a ranar Litinin, tare da tabbatar da

mutuwar mutum daya hudu suka jikkata tare da kuɓutar da sauran mutanen a yayin hadarin.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: