Kotun koli a Najeriya ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci a kan zaben shugaban kasa.

 

Kotun za ta yanke hukuncin ne dangane da korafin da tsofaffin yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun PDP Atiku Abubakar da LP Peter Obi.

 

An ayyana ranar Alhamis domin yanke hukuncin tare da kawo karshen kalubalantar zaben da su ke yi.

 

Daraktan yada labarai na kotun kolin Dakta Festus Akande ne ya tabbatar da haka a yau Laraba.

 

Kotun a ranar Litinin ta yi watsi da karar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APM bayan janyewa da yayi.

 

Idan ba a manta ba, a baya bayan nan, an yi takaddama dangame da takardun karatun shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar PDP ta yi zargin na jabu ne.

 

Batun da ya jawo cece ku ce har lokacin da makarantar ta fitar da bayanan karatun nasa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: