Rahotanni daga jihar Sokoto sun tabbatar da mutuwar yan bindiga da dama a karamar hukumar Tangaza a jihar.

 

An hallaka yan bindigan ne a ranar Talata da misalin karfe biyu na rana.

 

An kai harin kauyen Tukandu a karamsr hukumar Sakkwai a jihar.

 

Yan bindigan sun yi yunkurin kai harin ne da safiyar Takata, sai dai jami’an soji sun samu galaba a kansu.

 

Haka kuma sojin sun kwato babura 12 da bindiga kirar AK47.

 

Jami’an sun ce guda cikin sojin ya samu raunin harbi a jikinsa.

 

Gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya tabbatar da faruwar hakan.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: