Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga a yi gwanjon barikin ƴan sandan da ke faɗin Najeriya, don kawo ƙarshen wahalar rayuwa da jami’an suke ciki.

Kiran ya biyo bayan wani ƙudurin gaggawa da aka shigar gaban majalisar, wanda ɗan majalisa Murphy Omoruyi na jam’yyar LP ya shigar a yau Alhamis.

A yayin gabatar da ƙudirin ɗan majalisar ya ce, majalisar ta tabbatar da dokar aikin ƴan sanda ta shekerar 2020. Wacce tsohon shugaban ƙasa Buhari ya sanya wa hannu ranar 16 ga watan Satumbar shekerar 2020.

Omoruyi ya ce ɗaya daga muhimmin yin dokar shi ne, don samar da kyakkyawan yanayin rayuwa ga jami’an rundunar.

Ya ce a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020, gwamnatin tarayya ta kashe sama da Naira Biliyan 5 don gyaran barikokin. Amman duk wani ƙoƙari na gyaran ya ci tura.

Ya ce yanzu da jami’an ƴan sandan su ke rayuwa a cikin al’umma a maimakon barikokinsu, hakan yana tabbatar da muhimmancin samun intgantaccen tsaro da zaman lafiya.

Ya ce Amman duk da haka jami’an suna rayuwa ne a ruɓaɓɓun gidaje marasa kyau, wasu ma rufin su yana yoyo.

Kuma ana kallon jami’an ƴan sandan a matsayin masu cin hanci da rashawa, hakan kuma ya faru ne sakamakon yanayi marar kyau da rashin jin daɗi na rayuwa da su ke ciki. Duk sun rasa kima a cikin jama’a saboda halin rayuwar su mara kyau da suke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: