Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, tare da mashawarci na musamman akan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribado, sun yi wata ganawa a yau Juma’a domin tabbatar da tsaro a yayin zaben gwamnoni da za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da jihar Kogi.

 

Hukumar zaben a sanarwar da ta fitar ta ce ganawar ta shugabannin biyu tana da nasaba ne da kyakkyawan yunkurinsu na samar da muhimman abubuwan da za a yi amfani da su domin tabbatar da shiri na musamman na tunkurar zabubbukan jihohin wanda za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba mai kamawa.

 

Har ila yau zaman nasu ya tabbatar da cewa kwamitocin hukumar zabe na tsaro da shiga tsakani, ba za su bar kowace irin kofa ba wadda za ta haifar da samun matsalar tsaro a yayin zaben.

 

Cikin wadanda su ka halarci ganawar sun hada da kwamishinonin hukumar zaben na jihohi, sakataren hukumar zabe, daraktoci, da sauran ma’aikatan hukumar.

 

A yayin ganawar dai an tattauna muhimman batutuwa wadanda su ke da jibi da harkokin tsaro, sannan an fitar da hanyoyi da su ka dace domin yin zabukan cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da wata tangarda ba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: