Anan ma Rundunar sojin saman Najeriya ta Operation Whirl Punch ta kashe yan ta’adda da dama a cikin karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Daraktan yada labarai na rundunar sojin Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Gabwet ya ce jami’an sun kai harin ne da taimakon bayanan sirri da rundunar ta samu na cewa wani dan ta’adda mai suna Boderi da yaransa sun kafa sansani a cikin karamar hukumar.

Jami’in ya kara da cewa jamian sun hallaka mayakan ne ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai ta sama.

Ya ce hare-haren da jamian suka kai sun hallaka ‘yan ta’addan masu tarin yawa a yankin Doka da ke karamar hukumar ta Igabi a Kaduna.

Edward Gabkwet ya ce ‘yan ta’addan sun dade suna addabar mazauna kauyukan jihar ta Kaduna da kai hare-hare da yin garkuwa da mutanen yankunan.

Kakakin ya ce za su kara kaimi wajen yakar ‘yan ta’addan a ko ina suke afadan Najeriya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: