Majalisar Dattawa ta bakin Sanata Lawrence Ewurudjiako daga Jihar Bayelsa, bayyana duk sabon ministan da bai mika takardar dake dauke da bayanan yawan kadarorin da ya mallaka ba, to majalisa ba za a amince ta tabbatar dashi ba.

Lawrence Ya yi wannan bayani a jiya, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Majalisar

A cewarsa tun a cikin farfajiyar majalisar ya gabatar da hanzarin bayan kammala tantance tsohon ministan harkokin sufurin jiragen kasa, Hadi Sirika.

Sirika na daya daga cikin ministoci 43 da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada a zangon farko na mulkinsa kuma yanzu haka ya sake mika sunan sa a majalisar Dattawa.

Bayan Hadi Sirika ya fice Daga majalisar kasancewar ba’a yi Masa tambaya sakamakon ya taba zama Minista a zangon farko.
Nan take Sanata Lawrence ya ja hankalin majalisa a kan batun takardun rantsuwar dukiyar da mutum ya mallaka, wato ‘asset declaration’.

Ya ce wasu ministocin da ake tantancewa din ba su bayyana kadarorinsu ba tare da takardun rantsuwar dukiyar da suka mallaka ba.

A cewar Lawrence ya lura wasu babu satifiket na tabbatar da yawan Dukiyoyin da kadarorin da suka kawo shaidar mallaka, wanda hakan ya sabawa dokar kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: