Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Jihar.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa karar da dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP Aminu Bandel ya shigar ba ta da inganci.


Alkalin kotun mai shari’a Anyanwu ta bayyana cewa masu karar sun gaza gabatarwa da kotun abinda suke zargi a lokacin zaben.
Alkaliyar ta ce zarge-zargen da ake yiwa mataimakin gwamnan Abubakar Umar Tafida na samar da takardun bogi basu da tushe balle makama.
A yayin yanke hukuncin kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Kebbi, da ta yi watsi da karar da jam’iyyar ta PDP ta shigar gabata na mai kalubalantar nasarar gwamna Nasir.